✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk wanda ba ya kaunar Jihar Ribas kar ya sa rai da kuri’unmu —Wike

Wike ya ce a shirye jihar take wajen nuna wariya ga 'yan siyasa a zaben 2023.

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya sha alwashin cewa al’ummar jihar ba za su kada kuri’unsu ga ‘yan siyasar da ke kin jinin jihar ba.

Wike wanda ya sha kasa yayin neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya bayyana haka ne a ranar Litinin a yayin kaddamar da tashar jirgin ruwa ta Orochiri-Worukwo a jihar.

A cewar Wike, al’ummar Jihar Ribas a shirye suke su bijire wa makiyan jihar ta hanyar amfani da kuri’unsu a 2023.

Gwamnan ya jaddada cewa dole ne su ci moriyar duk wani dan takara da zai samu kuri’unsu.

Ya ce, “Idan ka ce Jihar Ribas ba ta da matsala, Jihar Ribas za ta ce maka ba ka da komai a lokacin da ya dace. Idan ba ku son mu, ba za mu so ku ba. Idan kuna son mu, za mu so ku.

“Babu wanda zai yi amfani da kuri’unmu a banza. Kuri’ar mu za ta yi tasiri kuma Jihar Ribas ta ci moriyar duk wanda za mu mara wa baya.

“Siyasa a yanzu ba ware wani dan takara ba ce a ce lallai sai shi za a zaba, ci gaban dai zai kawowa mutane shi ne abun la’akari.”

Aminiya ta rawaito cewa, ikirari na Wike na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar PDP a matakin kasa.

Bangaren Wike da kuma na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, sun shiga takun saka tun bayan daukar Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta da Atikun ya yi a matsayin abokin takara.