✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Duk wanda ya ba mu kudi za mu karba, mu zabi wanda muke so —Mutanen Osun

Masu jefa kuri'a a zaben Gwamnan Osun sun ce kudi ba zai sauya musu ra'ayi ba

Al’ummar Jihar Osun sun lashi takobin karbar kudin duk wani dan siyasa da ya yi musu tayi, kuma su zabi dan takarar da ransu ke so a zaben gwamnan jihar da ke gudana a ranar Asabar.

A safiyar Asabar dubban mutanen jihar suka domin duba sunayensu a jerin sunayen masu jefa kuri’a da jami’an Hukumar Zabe ta Najeriya (INEC) suka lika gabanin fara tantance da kuma jefa kuri’a.

A yayin da mastalar sayen kuri’u ta zama ruwan dare a zabukan Najeriya, masu zabe a jihar sun bayyana wa wakilanmu cewa ko wata-wata ba za su yi ba wajen amshe kudin ’yan siyasa masu neman kuri’u, amma idan suka tashi jefa kuri’a, gaban kansu za su yi.

Tun a ranar Juma’a aka girke jami’an tsaro iri-iri a manyan garuruwa da makwabtansu a jihar da ke da mutum akall 1,955,657 masu rajistae zabe.

Za a gudanar da zaben ne a rumfunan zabe 3,763 polling units a fadin jihar mai kananan hukumomi 30.

Zaben Gwamnan Osu

Zaben dai zai gudana tsakanin jam’iyyu 15, amma ana ganin zai fi zafi tsakanin gwamna mai ci, Gboyega Oyetola na Jam’iyyar APC da kuma Sanata Ademola Adeleke na Jam’iyyar PDP.

Karo na biyu ke nan da su biyun suke fafatawa a kan kujerar, wadda Oyetola ya lashe a zaben 2018 bayan ya kayar da Mista Adeleke.

Sauran manyan ’yan takarar su ne tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Wakilan Yusuf  Lasun na Jam’iyyar LP, Goke Omigbodun (SDP) da  Akin Ogunbiyi na Accord Party.

Fitowar masu zabe

Ana sa ran a wannan karon mutane za su fito sosai domin jefa kuri’a a zaben fiye da aben 2018, lokacin da mutum 767,444 ne suka kada kuri’a da cikin mutum 1,668,524 da ke da rajistar zabe a jihar a wancan lokacin.

Masu zabe a jihar dai sun bayyana cewa kudi ba zai sauya musu ra’ayi ba a wannan karon.

A zaben 2018 dai kashi 45.99 na masu karin zabe a jihar ne suka fito.

Gaban kanmu mu yi —Masu zabe

“ candidates of choice.”

Wani mazaunin jihar, Demola Ahmed, ya “In dai maganar sayen kuri’u ne, mutanen Osun wanda suke so su zaba, kuma duk dan siyasar da ya ba su kudi karbewa za su yi.

“Za a yi zaben ne ta hanyar la’akari da nagartar dan takara ba jam’iyyar sa ba.

“Mun wahala kuma mu gaji, shi ya sa muke so mu zabi wanda muke so kuma muke ganin zai biya mana bukatunmu.”

 

Daga: Sagir Kano Saleh, Abbas Jimoh (Abuja); Abiodun Alade, Hameed Oyegbade & Mumini AbdulKareem (Oshogbo)