✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk wanda ya biya ’yan bindiga kudin fansa za a daure shi shekara 15

Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu a kan sabuwar dokar.

Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu a kan dokar yanke hukuncin daurin shekara 15 ga duk wanda ya biya kudin fansa ga ’yan bindiga domin su wani da suka yi garkuwa da shi.

Da yake gabatar da kudurin a gaban Majalisar Dattawa, Sanata Ezenwa Francis Onyewuchi ya ce dokar ta shafi biyan kudi ta kuwace fuska ga ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da ’yan ta’adda domin su sako wanda suka yi garkuwa da shi.

“Duk wanda ya tura kudi ko ya biya ko ya hada baki ko ya shirya da masu garkuwa da mutane ko dan ta’adda wurin karbar kudin fansa domin sako wani mutum da suka yi garkuwa da shi, ya aikata laifin cin amanar kasa kuma za yanke masa hukuncin daurin akalla shekara 15 a gidan yari,” inji sabuwar dokar.

Sanata Ezenwa ya yi bayanin sabon tanadin sashe na 14 na Dokar Hukunta Laifukan Ta’ddancin ne, a lokacin da yake cewa ayyukan masu garkuwa da mutane na kara zama ruwan dare a Najeriya.

“Abubuwan da ake dora wa laifin yaduwar manyan laifuka su ne talauci da siyasa da ma addini ko rashin hukunta masu laifi da ma hadin bakin jami’an tsaro, rashawa da kuma son zuciya.

“Matasa mara aiki sun fara shiga harkar garkuwa da mutane a matsayin hanyar neman kudi, kuma abin da ya sa ake biyan kudin fansa shi ne tausayin wanda aka yi garkuwa da shi.

“Amma tarihi ya nuna ko da an biya kudin fansa, babu tabbacin wanda aka yi garkuwa da shi din zai fito lafiya,” inji shi.