✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk wanda ya karya dokar COVID-19 zai yi wata 6 a gidan yari

Mai kokarin hana tabbatar da dokar ma mai laifi ne kuma akwai hukunci

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan dokar da ta ayyana hukuncin daurin wata shida a gidan yari ga masu karya dokar COVID-19.

Sabuwar Dokar Kare Lafiya ta 2021 ta wajabta ba da zara a wuraren taruwar jama’a sannan wajibi ne kafin shiga, mahalarta su sa takunkumi, su wanke hannaye, a gwada zafin jikinsu da sauransu.

“Duk wanda aka kama ya karya daya daga cikin dokokin nan za a yi mishi tarara ko daurin wata shida a gidan yari ko a hada masa biyu”, inji sashe na 34 na sabuwar dokar.

Dokar ta kuma ayyana duk wanda ya hana wani ma’aikaci tabbatar da bin dokar kariyar COVID-19 a matsayin mai laifi kuma zai fuskanci hukuncin.

Ta kuma takaita yawan mahalarta a rufaffen wuri zuwa mutum 50, “sai dai a wuraren ibada, a nan kuma dole a takaita yawan zuwa rabin adadin da wurin ke dauka”.

Sannan kuma wajibi ne wuraren taurwar jama’a kamar makarantu, bankuna da wuraren ibada tabbatar da ganin mahalarta sun kiyaye dokokin kare yaduwar cutar COVID-19.

Duk da cewa akasarin tanade-tanaden dokar ba sabbi ba ne, amma dokar ta samar da cikakkiyar damar gurfanarwa da hukunta wadanda ake zargi da saba dokokin kariyar COVID-19.