✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko da a shirin fim mutum ya saki matarsa ta saku — Dokta Bashir

Ya bayar da fatawar cewa masa’ala ta aure da kuma saki babu wasa ko kadan a cikinta.

Babban Limamin Masallacin Al-Furqan da ke Unguwar Nasarawa G.R.A a birnin Kanon Dabo, Dokta Bashir Aliyu, ya yi fatawar cewa duk wani jarumin wasan kwaikwayo da ya yi furucin saki ga matasar ta cikin shirin fim, to kuwa a zahiri matarsa ta gaske ta saku idan har ya kasance yana da aure.

Dokta Bashir ya jaddada wannan matsaya ta fatawarsa yayin zanta wa da manema labarai ta hanyar wayar tarho, inda ya ce wannan ita ce hakikanin fahimtarsa a kan hukuncin da koyarwar addinin musulunci ta tanadar game da sakin matar aure.

Babban Limamin ya ce mas’ala ta fiqihun addinin musulunci ba ta kowane gama-gari bane ya yi fassara a kanta, sai dai fassara da kuma bayyana fahimta a kan kowace mas’ala ta kebanta ne kadai ga malamai masu ilimin addinin.

Wani hoton bidiyo da aka nada wanda a yanzu ya karade zaurukan sada zumunta da kuma yanar gizo, ya nuna babban malamin yayin da yake bayar da fatawar cewa masa’ala ta aure da kuma saki babu wasa ko kadan a cikinta kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Sai dai ko shakka babu wannan fatawa ta tayar da kura musamman a tsakanin masu amfani da zaurukan sada zumunta, inda da dama suka nuna kushensu a kai.

Fashin bakin da Dokta Bashir ya yi

Daga bisani Dokta Bashir ya sake fitar da wani hoton bidiyo inda ya yi karin haske dangane da fatawar da ya yi kuma ya yi mata lakabi da “cikakken bayani a kan hukuncin wanda ya saki matarsa da wasa.”

Ya ce, “Zan yi bayani ne zuwa ga jama’ar musulmi a kan bin da ya yadu a kafafiofin sada zumunta dangane da sha’anin saki da kuma abin da ya danganci ambatonsa a cikin wasan kwaikwayo.”

“Wannan magana ta zo a cikin darasi na tafsirin Al-Qur’ani da muke yi a masallacin Al-Furqan wanda ya zamto ta sanya rudani a cikin fahimtar mutane wanda ya wajaba ya zamanto na yi bayani saboda a saita fahimta kan abin da shi ne na ambata.”

“Da farko dai wannan magana ta zo a kan gaba ta bayanin tafsirin ayar Al-Qur’ani ta Suratul Taubah, wadda Allah yake cewa mazonsa, ka ce musu ya Rasulullah, Da Allah ne da ayoyinsa da Manzonsa kuka kasance kuna yi wa Izgili, to a kan haka ne na yi bayanin cewa izgili da wargi da wasa idan ya danganci janibin Allah da Al-Qur’ani da Manzon Allah SAW yana da hadari, domin zai fitar da mutum daga addini.”

“Sannan na ce izgili a kan abin da ya danganci hukunce-hukunce na shari’a, to shi ma akwai wani babi wanda yake da hadari, shi ne abin da ya danganci saki, da aure da komen aure, saboda Manzon Allah S.A.W yana cewa, abu uku gaskensu gaske ne, kuma warginsu ma gaske ne – saki da aure da kome.”

“To a kan haka ne, na ce idan mutum ya ce matansa na aure a cikin wasan kwaikwayo, wannan saki idan yana da matan a gaske, to wannan saki ya afku a kansu, sai dai maganar a dunkule take haka amma tana da tafsili (fashin baki).”

“Idan mutum a cikin wasan kwaikwayo ya kalli matarsa ta wasan kwaikwayo, ya ce, ke kin saku, ko ke wance na sake ki, to za a duba a gani, idan wannan matar wadda take cikin wasan kwaikwayon matarsa ce ta hakika tun kafin su yi wasan kwaikwayo ya zamanto da ita da shi duk suna shiri ne a cikin wasan kwaikwayon, to idan ya kalleta ya ce ya sake ta, duk da yake wasa ne, to wannan saki ya afku saboda wannan nassi na Hadisin Annabi S.A.W.”

“Amma idan wannan mata wadda take cikin wasan kwaikwayo ba matarsa ce ta aure ba, fim ne ko wasan kwaikwayo ne ya mayar da ita matarsa, to wannan saki bai samu mahalli ba, saboda haka matarsa ta aure babu abin da ya samu aurensa da ita.”

“Idan kuma ya zo yana bayar da labari ne a cikin shirin fim din, misali aka ce yana bayar da labari a wata fitowa a cikin shirin wanda ya zamto yana bawa abokanansa labari cewa, to ai ni matana ma gaba ki daya sun saku, ko ya ce, ai ni matata ma na sake ta, to wannan maganar da ya yi, matarsa ta aure duk da yake ba ita yake nufi ba, idan har yana da matar ta aure, to wannan saki ya afku a kanta, saboda wannan hadisi na Manzon Allah kuma saboda ayar Al-Qur’ani wadda Allah yake cewa, kada ku dauki ayoyin Allah su zama abin wasa kuma wannan ayar ta sauka ne a kan saki.”

“Saboda haka wannan ita ce maganar da na fada a dunkule, amma wannan shi ne tafsilinta, kuma wannan magana ta kan cewa wanda ya fada da wasa, abu ne wanda haka yake a Mazhabar Malikiyya, kuma haka yake Mazhabar mafiya yawan Malamai musamman Imamu Ahmad, wanda ya ce shi lafazin saki idan aka yi shi, ba a bukatar niyya, yana afkuwa ko mutum ya yi niyyarsa ko mutum bai yi niyyarsa ba.”

“To sai dai akwai malamai a Mazhabar Malik da suke cewa idan akwai wata karina (alama ko shaida) da take nuna wasa yake yi, to wannan shaidar za ta taimaka masa ta nuna kan cewa sakin bai afku a kansa ba.”

“To a bisa wannan, wadanda suka riga suka yi irin wannan fitowa a cikin wasan kwaikwayo, alal misali wani daga cikinsu yana da aure a ciki, yake bayani a cikin wasan kwaikwayo, yake cewa to ni na ma saki matata, to wannan tun da akwai shaidar kamar yadda aka ruwaito daga Ibn Al-Qassim duk da yake ba shi ne mashhurin mazhabar da ake fatawa a kai ba, to wannan ba zai bata aurensa ba, yana nan tare da matarsa.”

“Makasudin wannan shi ne a nunawa ’yan uwa wadanda suke cikin wannan sana’a ta harkar fim, kan cewa akwai (no go areas) abubuwa da ba za su yi ba, saboda tarbiyarsu ta addini, abin da ya danganci sifar Allah babu wasa da wannan; abun da ya danganci Al-Qur’ani, babu wasa da wannan, abun da ya danganci Manzon Allah S.A.W, babu wasa, babu izgili da wannan; abun da ya danganci aure da saki da kome, yin lafazi da su, babu wasu da wannan.

“To kowace al’umma tana da wuraren da aka yi mata shamaki, to ai ka ga duk wanda suke sha’anin harkar fim, sun san akwai wuraren da suke da iyaka, to mu ma saboda tarbiyarmu ta addinin musulunci,’yan uwa da suke cikin harkar fim, ya kamata su san irin wadannan iyaka da suka da ita, akwai wurare da ba a tsallake su ba a musu ketaresu, ai musu shamaki kada su ketar su je irin wannan wurare, wannan ita ce tarbiya ta addinin musulunci.

Kuma wannan maganar kamar yadda kuka gani, na gina ta ne a kan ayar Al-Qur’ani da Hadisin Manzon Allah SAW da kuma abin da shi ne mashhurin mazhabar Malik wanda a kansa fatawa take.”

Dokta Bashir a hoton bidiyon na tsawon minti bakwai, ya tuke da cewa, “Allah Madaukakin Sarki shi ne mafi sani.”