Daily Trust Aminiya - Duk wanda ya zagi Jonathan sai ya nemi yafiyarsa —Shehu Sani
Subscribe

Sanata Shehu Sani

Duk wanda ya zagi Jonathan sai ya nemi yafiyarsa —Shehu Sani

Sanata Shehu Sani, ya ce duk wanda ya zagi tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan saboda Shugaba Buhari ya nemi gafara.

A sakonsa kan cikar Jonathan —wanda ake wa lakabi da Maimalafa— shekara 63, Shehu Sani ya ce tun da Buhari ya tabbatar mai martaba ne, to duk masu zagin tsohon shugaban sun zalunce shi.

“Duk wanda ya zagi Maimalfa saboda Baba sai ya nemi yafiya wurin Maimalfa tunda yanzu Baba ma ya tabbatar cewa Maimalfa na da martaba, kun dauki alhakinsa ke nan”, inji shi.

Ya fadi haka ne sakon da ya wallafa a Facebook jim kadan bayan Shugaba Buhari ya fidda sakon taya Jonathan murnar cika shekara 63 wanda a ciki ya yabi gabacin nasa.

“Shugaba Buhari ya jinjina daukaka mai ban mamaki wadda ba kasafai akan ga irinta ba a fagen siyasar Najeriya da tsohon shugaban kasar ya samu, da kuma jajircewarsa wadda ta ba shi damar aiki a baya-bayan nan a matsayin manzon kungiyar ECOWAS na musamman wajen dawo da zaman lafiya a Jamhuriyar Mali”, inji sakon da Hadimin Shugaban Kasa kan Watsa Labarai, Femi Adesina ya fitar.

Daga karshe a sakon na Shehu wanda ya yi fice wurin caccakar ya kare sakon nasa da raha in da ya ce, “Zan dan taimaka maku da addu’an da zakuyi dan wanke kanku da tsarkake bakunan ku nan gaba.

“Sai dai kuna yawan son addu’a amma bakwa aiko da sadaka ko da na sayen tawada ne.

“A labarabce mukan kira irinku ‘Bani Bulusawa’ masu son na bulus kenan. Naku, Sheikh Algwagwarmawi”.

More Stories