✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dukkan alamu sun nuna PDP za ta lashe Legas a 2023 — Atiku

Ya ce PDP ba ta taba gangami a Legas irin wannan ba

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sha alwashin cewa jam’iyyarsa za ta lashe jihar Legas a babban zaben 2023 da ke tafe.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya yi wannan hasashe ne a ranar Talata yayin wani taron gangami na ’ya’yan jam’iyyar da aka gudanar a jihar don tunkarar zaben shekara mai zuwa.

Atiku ya kuma halarci turukan jam’iyyar ya kuma gana da ’yan takara da za su tsaya wa jam’iyyar zabe a mukamai daban-daban.

“Mu muka kafa jam’yyar PDP, amma tun da na soma harkar siyasa ban taba ganin yadda jihar Legas ta yi gangamin jama’a irin wannan ba,” in ji Atiku.

Dab takarar ya kuma ce wannan shi ya ba shi kwarin gwiwar cewa, babu shakka PDP ce za ta lashe zabe a jihar, don haka sai ya ce a shirye ya ke ya tallafa musu da duk abin da ya kamata domin samun nasarar. 

A na sa jawabin dan takarar Gwamnan jihar ya Legas a jam’iyyar, Dokta Olajide Adediran, ya yi alkawarin cewa Atiku za su yi, kuma babu gudu, babu ja da baya. (NAN)