✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duniya na cikin tsaka mai wuya —Gutteres

Muna wasa da bala’in sauyin yanayi. A kowane mako ana samun mummunan labari na sauyin yanayi.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce tarin matsaloli da suka yi wa duniya dabaibayi da suka hada da sauyin yanayi da yakin Rasha da Ukraine sun jefa duniyar cikin halin tsaka mai wuya.

Guterres wanda ya gabatar da jawabi a rana ta biyu na Babban Taron Tattalin Arzikin Duniya a Davos ya jaddada kalubalen da duniyar ke fuskanta na sauyin yanayi.

Sakataren ya bayyana cewa alkawarin da kasashe suka dauka na rage dumamar yanayi da maki daya da rabi a ma’aunin Celcius na nema ya gagari kundila.

“Ya ce muna wasa da bala’in sauyin yanayi. A kowane mako ana samun mummunan labari na sauyin yanayi.

“Gurbataccen hayaki na karuwa a sararin samaniya fiye da yadda ba a tsammani yayin da kudirin kasaashen duniya na takaita dumamar yanayin da maki daya da rabi a ma’aunin celcius yake neman zama al’mara.

“Idan ba dauki kwakkwaran mataki ba za mu doshi karuwar zafin da maki biyu da digo takwas a ma’aunin Celcius.”