✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duniya za ta fuskanci mummunan zafi idan… —WMO

Ana fargabar zafi zai karu zuwa mataki mai tsananin hadari.

Wani bincike da Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Duniya (WMO) ta gudanar ya gano cewa idan ba a yi da gaske ba, duniya na iya fuskantar matsanancin yanayin zafi sama da na yanzu, nan da shekara biyar masu zuwa.

Hukumar ta ce yanayin zafin zai iya karuwa da makin celcius 1.5 da ake kokarin kaucewa, wanda hakan ya sa aka shiga fargaba.

Masana kimiyya sun ce ko da sau daya a shekara aka samu yanayin da ya zarta maki 1.5, akwai babban hadari tare da narkewar kankara kan teku da kuma ambaliya.

WMO ta ce karya dokokin da aka kafa a yarjejeniyar sauyin yanayi na birnin Paris ko da sau guda ne, na iya haifar da matsalar da za a jima ana shan azaba na dumamar yanayi.

An jima dai ana gudanar da taruka kan shawo kan matsalar da ke kara haifar da dumamar yanayi, wanda kasashe suka dauki matakai daban-daban don magancewa.