✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

e-Naira: Abubuwa 9 da ya kamata ku sani a kan sabon kudin intanet

Kudin zai bambanta da sauran kudaden intanet na Cryptocurrency.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kirkiro da kudin intanet na e-Naira bayan ta haramta hada-hadar Cryptocurrency.

Kudin dai za su ba mutane damar hada-hadar cinikayya a tsakaninsu ta intanet.

CBN dai a baya ya ce ya dakatar da amfani da Cryptocurrency ne saboda ba wata kasa ce ta kirkiro shi a hukumance ba.

Za a dai kaddamar da fara amfani da kudin ne daga ranar daya ga watan Oktoban 2021.

Ga wasu daga cikin abubuwan da ya kamata ku sani a kan sabon kudin:

  1. Sabon kudin zai bayar da damar cinikayya, amma ya bambanta da kowanne irin kudi na intanet saboda hukuma ce za ta kirkiro shi ta hannun CBN.
  2. Kudin zai bambanta da sauran kudaden intanet na Cryptocurrency irinsu Bitcoin.
  3. Zai taimaka wa burin bankin wajen taimaka wa tattalin arziki da kuma taimaka wa rage amfani kudade na takarda.
  4. e-Naira, kudin da aka kirkira don hada-hadar intanet, ba ya bukatar kudade na zahiri.
  5. Darajarsu ba za ta rika hauhawar ba gaira ba dalili ba kamar na Cryptocurrency, kuma zai yi aiki kamar yadda Naira ta takarda take aiki.
  6. Kudin, darajarsu za ta kasance iri daya da ta Naira, kuma za su rika tafiya kafada da kafada.
  7. Za a kirkiri asusun ajiyarsu a banki daban da asusun ajiyar sauran kudade, kuma cibiyoyin hada-hadar kasuwanci ne za su bude asusun ta hanyar wata manhaja.
  8. Za su kasance halastattun kudade na kasa baki daya, ba za su rika amfani da kudin ruwa ba kuma CBN ne zai rika kula da hada-hadarsu da kuma iyakar abin da za a iya kashewa a kullum.
  9. Kasancewarsu muhimman kadarorin kasa, za a samar wa da kudaden cikakken tsaro, a kuma adana dukkan bayanan sirri na masu amfani da su saboda kaucewa masu kutse.