✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ebrahim Raisi ya zama sabon Shugaban Kasar Iran

Raisi zai zama Shugaban Iran na takwas tun bayan juyin-juya-halin kasar na 1979.

Dan takara nan mai ra’ayin rikau kuma jagoran bangaren shari’ar kasar Iran, Ebrahim Raisi ya lashe zaben Shugaban Kasar, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar ta sanar.

Raisi zai zama Shugaban Iran na takwas tun bayan komawar kasar tsarin jamhuriyar Musulunci a 1979.

Sakamakon zaben dai wanda aka fitar ranar Asabar ya nuna cewa Raisi ya samu kashi 61.95 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben ranar Juma’ah, inda kashi 48.8 na masu jefa kuri’a, adadi mafi wkaranci tun bayan juyin juya halin shekarar 1979.

Raisi ya samu kuri’a 28,933,004.

Tsohon Kwamandan Askarawan Juyin-Juya-Halin kasar, Mohsen Rezaei ne ya zo na uku da kuri’a 3,412,712 inda dan takara mai matsakaicin ra’ayi, Abdolnasswer Hemmati yake biye masa baya da kuri’a 2,427, 201, sannan mai tsaurin ra’ayin mazan jiya, Amir Hossein Ghazizadeh Hashemi da ya samu kuri’a 999,718.

“Babu wani abu na aikata ba daidai ba da aka fuskanta da zai shafi ingancin sakamakon zaben,” inji Ministan cikin gidan Iran, Abdolreza Rahmani-Fazli yayin taron manema labarai a Tehran.

’Yan takara Rezaei da Hemmati da Hashemi tun farko dai sun amince da shan kaye gabanin sanar da sakamakon zaben a hukumance ranar Asabar.

Raisi zai karbi mulki a watan Agusta daga hannun mai matsakaicin ra’ayin rikau Shugaba Hassan Rouhani wanda tsarin mulkin kasar bai ba shi damar sake tsayawa takarar karo na uku ba.

Raisi zai zama Shugaban Kasar Iran na farko da Amurka ta sanya wa takunkumi tun gabanin ya hau mulki duba da tun a shekarar 2019 Amurkar ta saka sunansa a jerin jami’an kasar da ta kakaba wa takunkumi.