✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS ta kakaba wa kasar Guinea takunkumi

ECOWAS ta ba wa sojojin wata shida su gudanar da zabe a kasar.

Shugabannin Kasashen Yammacin Afirka sun kakaba wa jagororin juyin mulkin kasar Guinea takunkumi, tare da bukatar a gudanar da zabe cikin wata shida don dawo da mulkin dimokuradiyya a kasar.

Wannan ya biyo bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Alpha Conde da sojojin kasar suka yi a farkon watan Satumba da muke ciki.

A wata sanarwar bayan taron, ECOWAS ta ce za ta kakaba wa sojojin da suka kifar da gwamnatin kasar da iyalansu takunkumin hana fita kasashen waje, tare da kwace kadarorinsu.

Ta yi kira ga kungiyar Tarayyar Afirka da Tarayyar Turai da su goyi bayan takunkumin da ta kakaba wa sojojin da suka yi juyin mulkin.

ECOWAS mai mambobi 15 ta riga ta dakatar da Guinea saboda juyin mulkin na ranar 5 ga watan Satumba, wanda Kanar Mamady Doumbouya ya jagoranta.

Juyin mulkin dai ya janyo damuwa a tsakanin kasashen duniya ganin yadda dimokuradiyya ke gamuwa da koma baya a Yammacin Afirka, musamman abin da ya faru a kasar Mali.

Sai dai a jawabinsa ga masu ruwa da tsaki a siyasar kasar, jagoran juyin mulkin Guinea, Kanar Mamady Dombouya, ya jaddada cewa gazawar ilahirin ’yan siyasan kasar ce ta tilasta musu hambarar da gwamnati.