✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS ta kara wa Guinea takunkumi kan rashin mika wa farar hula mulki

An dakatar da duk wani tallafin kudin da Guinea ta saba samu daga ECOWAS.

Shugabannin Kasashen Afirka ta Yamma sun dauki mataki haramta wa kasar Guinea tafiye-tafiye da kuma rike kadarorin kasar a yayin wani zaman gaggawa da suka gudanar.

A ranar Alhamis ce Kungiyar Bunkasa Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), ta amince da kakaba wa Conakry, babban birnin kasar takunkumi saboda kin yarda da tsayar da lokacin da mulkin kasar zai koma hannun farar hula.

Kazalika, sanarwar mai nasaba da babban taron da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a birnin New York na Amurka, ta dakatar da duk wani tallafin kudin da Guinea ta saba samu daga ECOWAS.

ECOWAS ta bai wa sojojin da ke rike da mulkin kasar wa’adin wata daya daga ran 22 ga Satumaba kan su shata lokacin da za su mika mulki ga farar hula ko kuma su fuskanci takunkumi mai tsanani.

Tun farko, ECOWAS ta ce wa’adin shekara biyu ta amince da shi kafin gudanar da zabe amma sojojin suka ce sai dai su yi shekara uku a mulkin kafin su yarda a gudanar da zabe.

Kasar Guinea mai fama da talauci duk da arzikin ma’adinai da take da shi, ta koma karkashin mulkin soji ne biyo bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a Satumbar 2021, inda suka hambarar da Shugaba Alpha Conde bayan shafe shekaru 10 rike da mulkin kasar.