✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS ta yi barazanar sake kakaba wa Mali sabon takunkumi

ECOWAS ta barazanar sake kakabawa Mali takunkumi.

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta jaddada takunkumin da ta dora wa gwamnatin mulkin sojin Mali bisa jinkirta mika mulki ga farar hula.

A karshen taron da ta yi Ghana, ECOWAS ta kuma yi kashedi ga sojojin da suka hambarar da gwamnatin kasashen Guinea da Burkina Faso.

Kungiyar, ta bukaci jagororin gwamnatin sojin Guinea da su gabatar da jadawalin mika mulki ga farar hula a karshen watan Afrilun da za a shiga, ko kuma su fuskanci sabbin takunkumai.

A wata sanarwa da ta fitar, ECOWAS ta sake jan kunnen sojojin da ke mulkin Burkina Faso da cewa idan ba su saki shugaba Roch Marc Christian Kabore da suka wa daurin talala ba zuwa mako mai zuwa, za a kakaba musu takunkumi.

Taron  da aka yi a babban birnin Ghana na Accra, na zuwa ne watanni uku bayan da kungiyar ta kakaba wa Mali takunkumi.

An ci gaba da yamutsa hazo sun bayan da dakarun sojin Mali suka hambarar da gwamnatin kasar tare da tsare shugaba Kabore.