✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS ta yi taron gaggawa kan juyin mulkin kasar Guinea

ECOWAS ta dakatar kasar Guinea daga jerin kasashen da ke cikin kungiyar.

Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika sun gudanar da wani taron gaggawa a kasar Ghana dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Guinea wanda ya kawar da zababben shugaban kasar, Alpha Conde, daga kan karagar mulki.

Tuni shugabannin karkashin kungiyarsu ta ECOWAS suka yanke hukuncin dakatar da kasar Guinea daga kungiyar sannan suka tura tawaga don tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulkin.

Yayin bude taron, Shugaban Kungiyar ECOWAS kuma Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya ce ana bukatar su da su yanke hukunci bayan sauraron bahasi daga tawagar wakilan da suka ziyarci Guinea, yayin da ya bukaci goyon bayan sauran shugabannin kasashen yankin 15 suka halarci taron.

Ministar Harkokin Wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, wadda ta jagoranci tawagar zuwa Guinea ta ce shugababbin sojin na da hurumin gabatar da shirin mayar da mulki ga fararen hula, amma kungiyar ECOWAS ce za ta yanke hukunci a kai.

Ana kuma sa ran taron zai saurari bayanai daga tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, wanda ke shiga tsakani wajen ganin sojojin da suka yi juyin mulki a Mali sun cika alkawarin da suka dauka na gudanar da zabe.