✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ECOWAS za ta hana shugabannin sojin Guinea sakat

ECOWAS ta ce za ta haramta wa jagororin juyin mulki taba kudinsu

Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ta ce za ta kakaba wa daidaikun jagororin juyin mulkin Guinea takunkumi.

Kungiyar ta ECOWAS, wadda ta bayyana haka ranar Alhamis, ta ce za ta haramta wa ko wanne daga cikin mutanen da suka yi juyin mulkin tafiye-tafiye, sannan ta bukaci a hanzarta mayar da kasar ta Guinea karkashin mulkin farar hula.

A wata sanarwar bayan taro da ta fitar, ECOWAS ta kara da cewa za ta kakaba haramcin ne a kan gungun sojojin da suka kifar da gwamnatin da iyalansu, sannan za ta haramta musu taba kudadensu da ke banki.

Shugabannin kasashen yankin Afirka ta Yamma ne suka yanke shawarar daukar wannan mataki yayin wani taron gaggawa da suka gudanar a birnin Accra na kasar Ghana.

A farkon wannan watan ne dai wasu sojojin kasar Guinea suka hambarar da Shugaba Alpha Conde.

Tuni dai kasashen duniya suka yi Allah-wadai da juyin mulkin, wanda Kanar Mamady Doumbouya ya jagoranta.