✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC na binciken yadda ’yan siyasa ke samun kudin fom din takara —Bawa

Bawa ya ce akwai bukatar a san tushen kudaden da ’yan siyasa ke sayen fom din takara.

Shugaban Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC), Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar ta fara binciken yadda ’yan siyasa ke samun kudaden da suke sayen fom din tsayawa takara.

Bawa, ya bayyana haka ne ranar Juma’a yayin tattaunawa a shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin na Channels.

“Idan aka zo batun sa ido kan kudaden zabe da kudaden ’yan takara, wannan na da alaka da aikin INEC, amma kuma muna aiki kafada da kafada da INEC da sauran hukumomin masu alaka a wannan fanni don tabbatar da cewa mun bi diddigin kudin.

“Muna so mu san tushen kudaden, na halas ne ko akasin haka,” in ji shi.

A cewarsa, EFCC na kokarin ganin ’yan siyasa sun yi amfani da kudin halak wajen sayen fom din takara a zaben 2023.

Kalaman na Bawa sun biyo bayan koken da jama’a suka yi kan farashin fom din takara na manyan jam’iyyun siyasa.

Jam’iyyar APC mai mulki ta sanya farashin fom din takarar shugaban kasa kan Naira miliyan 100, PDP kuma ta sanya nata miliyan 40, lamarin da ya jawo muhawara a tsakanin ’yan Najeriya.

Duk da cewa jam’iyyun biyu sun kare matakin nasu, ’yan Najeriyada masu lura da al’amura na ganin cewa fom din sun yi matukar tsada idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.

Wasu kuma na ikirarin cewa hakan zai iya haifar da babban hatsari ga tsarin dimokuradiyya tare da bude kofar yin sata ga ’yan siyasa don mayar da kudaden da suka saka kafin samun kujerar siyasa.

Sai dai shugaban na EFCC ya nanata kudurin hukumar na yaki da cin hanci da rashawa da tabbatar da gaskiya a tsarin zaben.

“Kun san mun damu da shugabanci na gari, mun ba da muhimmanci ga yin gaskiya.

“Muna kokarin ganin cewa ba a bai wa masu cin hanci mukaman shugabanci a kasar nan ba.

“Wannan yana daga cikin abubuwan da muke aiki a bayan fage don tabbatar da cewa an gano irin rawar da kowa ke takawa kafin samun kudin sayen fom din takara,” a cewar Bawa.

Har wa yau, ya ce EFCC na aiki tare da wasu hukumomi don tabbatar da samun sakamakon da ya dace a yaki da rashawa.