✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta cafke dalibai 30 masu damfara ta Intanet a Kwara

An nemi daliban su kauracewa wannan mummunar al’adar a matsayinsu na wadanda za su shugabanci kasar a gobe.

Ofishin Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa da ke Ilorin,  ya sanar da cafke wasu dalibai 30 da ake zargi da damfara ta yanar gizo, wadanda aka fi sani da ’yan Yahoo.

Ababen zargin wadanda mafi akasarinsu dalibai, an kama su ne a wurare daban-daban cikin birnin Ilorin, a cewar Babatunde Ayodele, Jami’in Hulda da Al’umma na hukumar a Jihar Kwara.

An yi nasarar kwato kaya a hannunsu da suka hada da manyan motoci na alfarma guda 10 da wayoyin salula da na’urorin kwamfuta kirar tafi-da-gidanka da layu da kuma wasu muhimman takardu.

Hukumar EFCC ta ce, nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da su a gaban kotu a yayin da take ci gaba da fadada bincike a kansu.

Hakumar ta ce, ta taba yi wa daliban gargadi kan damfarar mutane ta Intanet da sauran ayyukan laifi da ake aikatawa ta  yanar gizo a lokacin da aka gabatar da wata makala a wani taron wayar da kan daliban Jami’ar Al-Hikmah da ke Ilorin.

Shugaban da ke kula da ofishin EFCC shiyyar Ilorin, Usman Muktar, ya yi kira ga daliban da su kauracewa wannan mummunar al’adar a matsayinsu na wadanda za su shugabanci kasar a gobe.

Kazalika, ya shawarci daliban da su mayar da hankalinsu kan harkokin karatunsu sannan su kauracewa kutse da damfara ta shafukan Intanet da sauran laifuka makamancin wannan.