✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta gurfanar da Kabiru Tanimu Turaki a gaban kotu

Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati a Najeriya (EFCC) ta gurfanar da tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Tanimu Turaki, a…

Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati a Najeriya (EFCC) ta gurfanar da tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Tanimu Turaki, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa zargin almundahana.

Hukumar ta gurfanar da tsohon ministan ne a gaban mai shari’a Inyang Ekwo tare da tsohon mai taimaka masa na musamman, Sampson Okpetu, da wasu kamfanoni guda biyu, Samtee Essentials Limited da Pasco Investment Limited, bisa zargin yin amfani da kamfanonin wurin karkatar da wasu kudade.

Turaki bai amsa zarge-zargen ba a gaban kotun.

Alkali Inyang Ekwo ya amince da bukatar beli wadda lauyan wanda ake karar ya gabatar bisa sharuddan da kotun ta gindaya wadanda suka hada da haramta wa wanda ake tuhumar yin bulaguro zuwa kasar waje ba tare da izinin kotun ba.

Alkalin ya dage zaman sauraren shari’ar zuwa 22 ga watan Yuni.

Kamfanin Dillancin Labarai ta Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Turaki, wanda babban lauya ne, ya rike mukamin ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati daga shekarar 2013 zuwa 2015 kuma yayi aiki a matsayin minista mai kula da harkar kwadago daga shekarar 2014 zuwa 2015.