✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama Fani-Kayode a kotu, ta wuce da shi ofishinta

Matakin dai na zuwa ne mako daya bayan hukumar ta kama shi.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) a ranar Talata ta kama tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode a Jihar Legas.

Rahotanni sun ce jami’an hukumar sun kama shi ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Ikoyi a Jihar Legas, sannan suka wuce da shi ofishinta.

Daga nan ne kuma suka wuce da shi zuwa ofishin hukumar da ke Jihar.

Tsohon Ministan dai wanda bai jima da komawa jam’iyyar APC mai mulki ba an gurfanar da shi ne a gaban kotun kan zargin yin amfani da takardun bogi a kan shari’ar da ake yi masa.

Bayan kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Janairun 2022, an dai hango shi yana tafiya, kafin wani jami’in bincike na EFCC ya kama shi sannan aka yi awon gaba da shi.

Wani jami’in bincike a hukumar ta EFCC, ya tabbatar da kamen, inda ya ce yanzu haka yana can yana amsa tambayoyi ne kan zargin gabatar da takardun karya kan lafiyarsa, don ya kauce wa gurfana a gaban kotun.

Matakin dai na zuwa ne mako daya bayan hukumar ta kama shi kan makamancin wannan zargin.