✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama masu damfara ta Intanet 92 a Fatakwal

EFCC ta ce ta kuma kama wasu mutane 39 a birnin Ibadan na Jihar Oyo.

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa arzikin kasa zagon kasa a Najeriya, ta ce ta yi nasarar cafke mutum 92 wadanda take zargi da gudanar da ayyukan da suka shafi damfara ta yanar gizo a birnin Fatakwal na Jihar Ribas.

Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma’a ta ce, da sanyin safiyar ranar Laraba, jami’anta suka yi wa mutanen dirar mikiya a wurare daban-daban na jihar ta Ribas.

“Mun kama mutum 92 da ake zargi da aikata ayyukan damfara a wuraren da suka hada da Choba da Ada George a birnin Fatakwal da ke Jihar Ribas,” a cewar sanarwar.

Hukumar ta EFCC ta ce ta samu nasarar cafke mutanen ne wadanda ake kira “Yahoo Boys” bayan wasu bayanan sirri da ta tattara.

Ta kara da cewa, na’urorin da aka kwace a hannun mutanen da ake zargin, sun nuna cewa 64 daga cikin mutum 92 na da hannu dumu-dumu a ayyukan na damfara.

A wani labari makamancin wannan, hukumar ta EFCC ta ce ta kuma kama wasu mutane 39 a birnin Ibadan na Jihar Oyo da ke Kudancin kasar, wadanda su ma take zarginsu da ayyukan damfara ta yanar gizo.