Daily Trust Aminiya - EFCC ta kama shugaban hukumar tsara birane ta Kaduna

Jami’an EFCC a bakin aiki

EFCC ta kama shugaban hukumar tsara birane ta Kaduna

Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC a ranar Litinin sun yi dirar mikiya a shalkawatar Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA), sannan suka yi awon gaba da shugabanta, Malam Ismail Umaru Dikko.

Hukumar KASUPDA dai ta yi fice a Jihar Kaduna a matsayin hukumar gwamnatin da aka fi tsoro saboda yadda take rushe-rushe a Jihar.

Kafin nadinsa shugabancin hukumar, Malam Sama’ila dai ya taba zama mai taimaka wa Gwamna Nasiru El-Rufa’i, daga bisani kuma aka daga likafarsa zuwa shugabancin KASUPDA a shekarar 2019.

Aminiya ta gano cewa EFCC ta yi wa hukumar kawanya ne sannan ta kama shi lokacin da yake tsaka da taro da ma’aikatansa, ’yan mintuna kadan bayan karfe 10 na safe.

Wani ganau a wajen ya ce an dan sami hatsaniya a hukumar kafin daga bisani su saka shi a bakar mota kirar Hilux ta jami’an na EFCC.

A cewar wasu majiyoyi, jami’an na EFCC sanye da bakaken kaya dauke da bindigogi sun yi awon gaba da shi sannan suka raka shi zuwa cikin motarsu.

Sun ce da farko ma’aikata da jami’an tsaron hukumar sun yi yunkurin hana tafiya da shi, amma shugaban ya umarcesu su bari a tafi da shi.

Wakilinmu ya gano cewa an wuce da shugaban ne zuwa ofishin shiyya na hukumar da ke Kaduna, bayan da a baya ya ki amsa gayyatar da hukumar ta sha yi masa.

Karin Labarai