✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda EFCC ta kama tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari

Wasu kafofin yada labarai sun ce da maraicen Lahadi aka kama tsohon gwamnan

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta yi awon gaba da tsohon Gwaman Zamfara, Abdulaziz Yari.

Wata majiya majiyoyi a Hukumar ta shaida wa wakilin Daily Trust cewa an kama tsohon gwamnan ne bisa zargin ya sharbi romon almundahanar da aka ce Akanta Janar na Tarayya Ahmed Idris.

“Ranar [Lahadi] 29 ga watan Mayu EFCC ta kama Yari da Anthony Yaro, Shugaban kamfanin Finex, saboda rawar da ake zargin sun taka a badakalar Naira biliyan 84 da ta zargo tsohon Akanta Janar na Tarayya.

“Ana zargin cewa Yari, wanda aka kama da misalin karfe 5 na yamma, ya amfana da Naira biliyan 22 daga cikin kudin, wanda tsohon Akanta Janar din ya bai wa wani mutum mai suna Akindele, ta hanyar Finex Professional”, inji majiyar.

Bayanan sirri

Idan ba a manta ba, kusan mako biyu da suka wuce aka kama Akanta Janar din na Tarayya ana zargin cewa ya amince da wasu kwangiloli na bogi, wadanda ta hanyarsu, inji EFCC, ya yi ruf-da-ciki a kan makudan kudaden.

Hukumar ta kuma ce ta gano kadarori akalla 17 da ya mallaka ta hanyar haram.

“Tabbatattun bayanan sirri na Hukumar sun nuna cewa AGF din ya ribaci kudin ne ta hanyar kwangilolin bogi da sauran haramtattun ayyuka, yana mai amfani da ’yan aike da danginsa da wasu na hannun damansa.

“An kuma yi kokarin halalta kudaden na haram ta hanyar sayen kadarori a Kano da Abuja”, inji EFCC.

Jaridar The Punch ta ruwaito wani jami’i a Hukumar yana cewa an gano kadarorin da Akanta Janar din ya mallaka a Kano da Legas da Abuja da Dubai da Landan.

A makon jiya ne dai Gwamna Abdulaziz Yari ya lashe zaben fid-da-gwani na jam’iyyar APC a Jihar Zamfara don yin takarar dan Majalisar Dattawa.

Yari da Sanata Kabiru Marafa sun samu tikitin takarar ne ba hamayya sakamakon wata yarjejeniya da aka cimma tsakaninsu da Gwamna Bello Matawalle.