✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kama ’yan Yahoo Boys 150 cikin wata biyu

EFCC ta yi wawan kamu na masu damfarar mutane ta Intanet a Ibadan.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) da ke Ibadan ta ce, ta kama mutum 143 mafi yawanci matasa ’yan Yahoo Boys da ake zargi da laifin damfarar mutane da kamfanoni dubban miliyoyin Naira ta Intanet.

Bayanin haka na kunshe ne a takardar sanarwa biyu da Kakakin Hukumar, Wilson Uwujaren ya sanya wa hannu da aka raba wa ’yan jarida a Ibadan.

Sanarwar farko ta ce, jami’an hukumar sun kama mutum 80 a sassan Ibadan hedikwatar jihar, yayin da shiyyar hukumar ta Enugu ta kama mutum 40.

Sanarwa ta biyu kuwa cewa ta yi kamen ya rutsa da mutum 23 a unguwannin rukunin gidaje na Apata da Jericho da Ire-Akari duk a birnin Ibadan.

Wilson, ya nuna wasu daga cikin hotunan wadannan mutane da motocin alfarma da wayoyin salula masu tsada da kwamfutoci da kudade da aka samu tare da su a lokacin kamen.

An gurfanar da wadansu daga cikinsu a gaban kotuna daban-daban a karkashin hurumin hukumar domin yanke musu hukunci kan laifin da ake zargin sun aikata a yayin da ake ci gaba da bincike a kan sauran.

An gurfanar da wani dan kasar Indiya mai suna Yubraj Kumar Mehra a gaban Babbar Kotun Jihar Ogun, inda aka tuhume shi da kamfaninsa na Dolphins Steeles Nigeria Limited da laifin bayar da cak din kudi na bogi har sau 13 na jimlar Naira miliyan 125 a tsakanin watan Oktoba da Disamban shekarar 2018 ga Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan (IBEDC).

Alkalin kotun, Mai shari’a Olanrewaju Majekobe ta bayar da belin Yubraj Kumar Mehra a kan Naira miliyan biyu da rabi.

A kwanan baya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa Shugaban Hukumar EFCC a kan nasarar kwato Naira biliyan 152 da Dalar Amurka miliyan 85.