✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta kwato N1bn a hannun jami’in gwamnati

EFCC ta bayyana yadda ta gano kudin a asusun bankin ma'aikacin gwamnatin.

Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC), ta kwato N1bn daga hannun wani ma’aikacin gwamnati da ba a bayyana sunansa ba.

Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka a loakcin da ya bayyana a gaban kwamitin Majalisar Dattawa  kan Kudaden Shigan Hukumomin Gwamnati.

“Akwai abubuwa da dama da muke bukatar tsohewa ba wai iya kudaden shiga ba kadai, saboda ko a makon jiya sai da muka kwato Naira biliyan daya a hannun wani ma’aikacin gwamnati,” a cewarsa.

Ya ce a makon da ya gabata ne aka gano kudin da ke ajiye a asusun bankin ma’aikacin gwamnatin.

Bawa ya ce EFCC za ta amince da rahoton kwamitin da za su gabatar da zarar sun kammala bincike kan lamarin.

“Na yi farin ciki kan yadda na ga kwamitin na gudanar da binciken.

“A wannan lokacin, kasar nan ba wai iya kudaden shiga kadai za ta toshe hanyoyin zurarewarsu ba, har hanyoyin da ake samun kudaden ya kamata a toshe su,” cewar Bawa.