✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta sake gano Dala miliyan 72.8 a asusun bankin Diezani

EFCC ta bankado kudaden a wani asusun ajiyarta da ke bankin Fidelity.

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta sake gano Dalar Amurka miliyan 72.8 a wani asusun ajiyar bankin tsohuwar Ministar Albarkatun Mai, Diezani Alison-Madueke.

EFCC ta ce ta gano kudaden ne a asusun Diezanni da bankin Fidelity a Najeriya.

Bayan haka kuma hukumar ta cafke tsohon daraktan bankin mai suna Nnamdi Okonkwo, wanda a yanzu na daya daga shugabannin bankin ‘First Bank’ wanda a baya ya sha tambayoyi kan Dala miliyan 153 da kuma Dala miliyan 115.

Duk da cewa EFCC ta karbi Dala miliyan 153, har yanzu batun Dala miliyan 115 da ake zargin shi a kansu na gaban kotu.

A yanzu dai Mista Okonkwo da Charles Onyedibe na hannun EFCC inda suke amsa tambayoyi kan Dala miliyan 72.8 da aka samu a asusun Diezani.

Ko a watannin da suka gabata sai da Gwamnatin Tarayya ta yi gwanjon wasu kadarorin da ta gano daga Diezani.

Tun bayan saukar ta daga kujerar minista, Diezani ke shan tuhume-tuhume kan zargin badakala da dukiyar kasa.