✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta saki tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilai Patricia Etteh

Ita ce mace ta farko a Najeriya da ta taba jagorantar majalisar a tarihi.

Bayan shafe kwanaki uku a komar Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya, tsohuwar shugabar Majalisar Wakilai, Patricia Etteh ta shaki iskar ’yanci.

A wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya fitar, ya ce tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilan ta shaki iskar ’yancin ce a ranar Juma’a.

Uwujaren ya ce an sako Misis Patricia ce bayan ta cika sharudan bayar da beli, inda aka gindaya mata sharadin gabatar da kanta daga lokaci zuwa lokaci domin ci gaba da gudanar da bincike.

Yadda EFCC ta cafke Patricia Etteh

A makon da ya gabata ne Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki ta’annati, ta kama tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilai.

An ruwaito cewa EFCC ta yi awon-gaba da Misis Etteh ne kan zargin almundahanar kudade a Ma’aikatar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) da yawansu ya kai Naira miliyan 287.

Wata majiyar EFCC ta ce ana zargin Misis Etteh ta karbi Naira miliyan 130 ta Kamfanin Phil Jin Project Limited da NDDC ta bai wa kwangilar Naira miliyan 240 a 2011.

Hukumar EFCC ta nemi ta yi bayanin shigar kudin asusunta amma ta gaza fadar komai a kai.

“Etteh ba darakta ba ce ko ’yar kwangila, saboda haka me ya kai wannan kudin asusunta. A kan haka muke bukatar ta yi bayani kuma kawo yanzu ba ta yi ba,” inji majiyar.

An zabi Patricia Etteh a matsayin Shugabar Majalisar Wakilai a 2007, to amma ta yi murabus ne bayan ’yan watanni bisa zargin karkatar da wasu kudade.

’Yan majalisa a lokacin sun yi barazanar tsige ta daga Shugabar Majalisar kafin ta yanke shawarar sauka da kanta.

A wancan lokaci ana zarginta da ware wasu makudan kudi don ba da kwangilar gyaran gidan Shugaban Majalisar Wakilai amma aka karkatar da su.

Ita ce mace ta farko a Najeriya da ta taba jagorantar majalisar a tarihi.

Kamen nata na zuwa ne kwana kadan bayan da EFCC ta kama Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, bisa zargin sama da fadi da Naira biliyan 80.

Hukumar EFCC ta ce ta kama shi ne bayan ya ki amsa gayyatar da ta yi masa don amsa wasu tambayoyi.

Wadansu ’yan Najeriya sun rika tsokaci kan kama Akanta Janar din da zargin wawushe biliyoyin Naira, bisa la’akari da cewa yana rike da babbar kujera a gwamnatin Shugaba Buhari da ke ikirarin yaki da cin hanci da rashawa.