✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta titsiye Kwankwaso kan badakalar kudaden fansho

Ana dai zarginsa ne da yin babakere a kan wasu kudaden fansho har N10bn.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta titsiye tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kan zargin badakalar kudaden fansho.

Rahotanni sun ce hukumar ta gayyace shi ne bayan wani korafi da wasu ’yan fanshon suka kai gabanta.

Wani jami’i a hukumar ya tabbatar wa Aminiya cewa Sanata Kwankwaso ya amsa gayyatar ta EFCC, inda ya ce, “Yana amsa tambayoyi ne kan jerin korafe-korafen da aka shigar a kansa kan zargin yin babakere a kan kudaden fansho lokacin da yake Gwamnan Kano.”

A daya daga cikin irin wadannan korafe-korafen dai, ana zargin tsohon Gwamnan na Kano da karkatar da kudaden na ’yan fansho wajen gina gidaje da yawansu ya kai Naira biliyan 10, amma ya sha musanta hakan.

Har yanzu dai EFCC ba ta magantu ba a kan lamarin, amma a baya ta ce tana tuhumarsa ne kan wasu kudaden Kananan Hukumomin Jihar da yawansu ya kai N3.08bn.