✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC ta tsare Tanko Al-Makura kan zargin rashawa

EFCC ta cafke tsohon gwamnan kan zargin badakala.

Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta cafke tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura da matarsa kan zargin rashawa.

Rahotanni a ranar Laraba sun tabbatar da cewar yanzu haka ana rike Al-Makura da matarsa a ofishin EFCC da ke Birnin Tarayya Abuja.

  1. Mutum 5 sun mutu bayan fashewar bam a Jamus
  2. ‘Buhari ya fi shekara 40 yana zuwa Landan a duba lafiyarsa’

Bayanai sun ce hukumar ta cafke Sanata Al-Makura kan zargin yadda aka karkatar da akalar wasu kudade a lokacin da ya mulki Jihar Nasarawa na tsawon shekara takwas.

Al-Makura ya mulki Nasarawa daga shekara ta 2011 zuwa 2019 kafin daga bisani ya tafi Majalisar Dattawa a matsayin Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu.

Sai dai ya zuwa yanzu EFCC ba ta fitar da wata sanarwa dangane da cafke tsohon gwamnan ba.