EFCC za ta biya miliyan N20 kan tsare wani ba bisa ka’ida ba | Aminiya

EFCC za ta biya miliyan N20 kan tsare wani ba bisa ka’ida ba

Kotun ci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), tarar Naira miliyan 20 saboda tsare tsohon Daraktan bankin First Bank, Dauda Lawan, ba bisa ka’ida ba.

Kotun ta umarci EFCC ta biya tarar ne a matsayin diyya ga Dauda Lawan, saboda tsare shi da hukumar ta yi na awa 24 ba bisa ka’ida ba.

Alkalin Kotun, Sule Muslim Hassan, a lokacin da yake yanke hukuncin ya ce EFCC ta gaza ba wa kotun kwakkwaran dalilinta na tsare Dauda Lawal.

Ku biyo mu do karin bayani.