✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EFCC za ta daukaka kara kan hukuncin kotu na wanke Babachir

EFCC ba ta gamsu da hukuncin wanke Babachir da kotu ta yanke ba shi ya sa ta ce za ta daukaka kara.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta wanke tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal daga zargin karkatar da miliyan N544.

EFCC ta gurfanar da Babachir a kotu ne inda take tuhumar sa da laifuka guda 10.

Aminiya ta rawaito ana zargin tsohon Sakataren ne tare da kaninsa Hamidu David Lawal da Suleiman Abubakar da Apeh John da kuma wasu kamfanoni biyu.

Zargin da ake yi musu ya hada da karkatar kudi miliyan N544 da gwamnati ta ware don aiwatar da aiki a yankin Arewa maso Gabas.

Sa’ilin da yake yanke hukunci a zaman kotun a ranar Juma’a, Alkalin kotun Mai Shari’a Agbaza ya ce, duka shaidu 11 da EFCC ta gabatar wa kotun ba su nuna an aikata wani laifi ba.

Don haka Kotun ta yanke hukunci cewa an kayar da EFCC a shari’ar bayan ta gaza gamsar da kotu da hujjoji.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne, ko EFCC za ta yi nasarar a karar da ta ce za ta daukaka din.