✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar Ekweremadu ya koma APC

Ana zargin janyewar na da alaka da rikici tsakanin Ekweremadu da Gwamnan Ugwanyi da shugabancin PDP kan karba-karba

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ike Ekweremadu, ya janye daga neman tikitin takarar Gwamnan Jihar Enugu a jam’iyyar PDP.

Ekweremadu wanda tun 2003 yake Majalisar Dattawa, ya sanar da janyewarsa ce ranar Laraba, sa’o’i kadan kafin fara zaben fitar da dan takarar gwaman PDP a jihar.

Daraktan Yada Labaran kungiyar yaken neman zaben Ekweremadu, Charles Asogwa, ya ce, “Muna sanar da magoya baya da sauran al’ummar Najeriya cewa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, kuma babban mai neman takarar Gwamnan Jihar Enugu, Sanata Ike Ekweremadu, ya janye daga zaben fitar da dan takarar gwamnan PDP daga yau Laraba, 25 ga watan Mayu, 2022.”

Ana zargin Ekweremadu ya dauki matakin ne a wani yunkuri na komawa jam’iyyar APC.

Tun a ranar Talata alamu suka fara bayyana na yiwuwar komawarsa APC, domin neman kujerar Gwamnan Jihar Enugu a zaben 2023.

A ranar aka gan shi a ofishin yakin neman zaben APC da ke Abuja, inda aka yi wata tattaunawa da shi da ake ganin yunkuri ne na kammala shirinsa na dawowa APC da nufin kayar da PDP a zaben gwamnan jiharsa a 2023.

Kafin wannan juyin wainar, Uche Nnaji shi ne APC ta yi masalaha a kansa, a matsayin dan takararta na gwamnan jihar.

Sai dai ana ganin idan har tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar ya koma APC, da alama Mista Nnaji ya fice janye neman takararsa.

Dalilin janyewar Ekweremadu

Duk da cewa sanarwar ba ta bayyana dalilin janyewar Ekweremadu ba, ana ganin hakan na da alaka da yakin cacar baki da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Enugu mai ci, Ifeanyi Ugwuanyi da shugabancin PDP na jihar kan tikitin takarar gwamna a zaben 2023.

Gwamna Ugwanyi da jam’iyyar PDP mai mulkin Jihar Enugu, sun sha alwashin bin tsarin karba-karba na kujerar gwamna a jihar domin tabbatar da daidaito da adalci a tsakanin bangarorin jihar.

A baya-abyan nan PDP ta sanar cewa ta bai wa yankin Enugu ta Gabas takarar kujerar gwamnan jihar.

Amma Ekweremadu, dan asalin yankin Aninri da ke Enugu ta Yamma ya sha yankar tikitin takarar neman kujerar gwamna, sabanin yarjejeniyar, wadda ya ca ba a taba yi ba.

Idan ba a manta ba, bayan zaben daliget din kananan hukumomi da PDP ta gudanar a ranar 30 ga watan Afrilu a Jihar Enugu, wansu magoya bayan Ekweremadu sun shigar da kara suna neman kotu ta soke zaben.

Sai dai Babbar Kotun Tarayyar da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da karar ta kuma tabbatar da daliget uku da aka zaba a kowanne daga gundumomi 260 da ke jihar domin zaben ’yan takarar zaben 2023 a jihar.

A zaben fitar da ’yan takarar Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jihar Enugu, babu ko mutum daya da ya yi nasara daga bangaren Ekweremadu.

Daga baya ya shirya nashi taron jam’iyya inda aka zaben ’yan takararsa a matsayin wadanda suka samu tikitin jam’iyyar.