✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El Clásico: Ana dauki ba dadi tsakanin Real Madrid da Barcelona

Ko wacce kungiya na matukar bukatar makin ukun da za a iya samu daga wasan

A yau Asabar za a fafata wasa a tsakanin kungiyoyin Real Madrid da Barcelona, a wani wasa da masu sha’awar kwallon kafa ke ganin za a sha kallo duba da muhimmancinsa da kuma bukatar maki da ko wanne kulob ke da ita a karon battar.

El Clásico wasa ne da ake fafatawa a tsakanin kungiyoyin Real Madrid da Barcelona.

A da can ana kiran wasan da aka buga tsakanin kungiyoyin guda biyu a wasan Laliga ne kawai, amma daga baya aka hada da duk wasannin da suka buga a ko wacce gasa.

An buga El Clásico na farko ne a ranar 13 ga watan Mayun 1902, inda kungiyar Barcelona ta lallasa Real Madrid da ci uku da daya.

A haduwarsu ta karshe kuwa, Real Madrid din ce ta lallasa Barcelona da ci ukun da daya a Camp Nou a ranar 24 ga watan Oktoban bara.

Dalilin matukar muhimmancin wasan

A yanzu haka Atletico Madrid ce a saman teburi da maki 66, sai Barcelona ta biyu da maki 65 sai Real Madrid ta uku da maki 63.

Ke nan idan Real Madrid ta doke Barcelona a yau, za ta iya komawa ta farko idan aka yi la’akari da bambancin kwallaye kafin Atletico Madrid ta buga nata wasan.

Idan kuma Barcelona ta doke Madrid, za ta hada maki 68. Ke nan za ta hau saman teburi da tazarar maki biyu kafin Atletico Madrid ta buga wasa.

Idan kuma Atletico Madrid ta yi rashin nasara, duk kungiyar da ta lashe El Clásico din za ta dare saman teburi.

Idan kuma Athletico Madrid ta yi kunnen doki, Barcelona za ta hau saman teburi idan ta ci wasan, amma ko Madrid ta samu nasara ba za ta hau ba.

Wannan ya sa wasan zai yi zafi.

Sai dai masu sharhi a kan wasanni suna ganin kungiyar Barcelona tana yayi a kwanakin nan, sannan kuma Sergio Ramos da Varane na Madrid ba za su buga wasan ba.

Amma a wasa irin wannan, ba a sanin maci tuwo, sai miya ta kare.