✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai da Kungiyar Kwadago sun sa zare a Kaduna

Yajin aikin zai gurgunta dukkanin al’amura da ayyukan tattalin arziki a fadin Jihar.

An sa zare tsakanin Gwamnati da Kungiyar Kwadago a Jihar Kaduna, yayin da kungiyar ta bai wa dukkanin ’ya’yanta umarnin shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar a fadin Jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan yajin aikin zai gurgunta dukkanin al’amura da ayyukan tattalin arziki ciki har da na fannin zirga-zirgar jiragen sama, bangaren lantarki, bankuna da harkokin man fetur a Jihar.

Sauran wadanda yajin aikin zai shafa sun hada da ma’aikatan jinya da na unguwar zoma, kungiyar ma’aikatan ilimi marasa karantarwa, ma’aikatan gidajen rediyo da na talibijin da sauransu.

A kan haka ne Shugaban Kungiyar Kwadago na Kasa, Kwamared Ayuba Wabba da sauran Shugabannin Kungiyar a fadin Tarayya za su tabbatar da shiga yajin aikin da aka tsara zai fara daga karfe 12 na daren Asabar.

Kwamared Wabba ya ce matakin hakan wanda ya zama tilas na zuwa ne domin yi wa gwamnatin Jihar matsin lambar sauya hukuncin da ta yanke na korar ma’aikatanta fiye da dubu hudu da Gwamna Nasir El-Rufai ya yi.

Sai dai Gwamnatin Jihar a wata sanarwar da ta fitar ranar Asabar, ta ce ba za ta hana tafiya yajin aikin ba, amma dokar kungiyar ta yi bayani karara kan haramta wa ma’aikatan da aikinsu ya zama wajibi shiga yajin aiki.

Sanarwar da Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar da Shugabar Ma’aikatan Jihar, Jafaru Ibrahim Sani da Hajiya Bara’atu Muhammad suka fitar, ta ce Gwamnati ba ta bari a yaudare ta da wannan yajin aiki ba.

Hakan kuma, sanarwar ta ce Gwamnatin za ta sanar da jami’an tsaro su dauki mataki kan wadanda suka shirya yajin aikin tare da zanga-zangar da ake ganin za ta iya rikidewa zuwa tashin hankali.

“Baya ga batun dokar annobar Coronavirus wadda aka gindaya domin haramta gudanar da manyan taruka a Jihar Kaduna, an kuma sanya wannan doka ne saboda dakile irin wadannan tarukan da ko an fara su cikin ruwan sanyi suke rikidewa su koma rikici,” a cewar sanarwar.