✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai na neman Shugaban NLC ruwa a Jallo

NLC na yajin aiki saboda sallamar ma'aikata da El-Rufai ke yi.

Gwamnann Jihar Kaduna ya ayyana Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC), Ayuba wabba, a matsayin wanda ake nema ruwa a Jallo.

El-Rufai ya sanar da haka ne a safiyar Talata, washegarin fara yajin aikin gargadi na kwana biyar da Ayuba Wabba ya jagoranci farawa a Jihar Kaduna, kan korar ma’aikata da Gwamnatin El-Rufai ke yi.

Yajin aikin da zanga-zangar ta NLC ta gurgunta harkoki a fadin Jihar Kaduna, inda aka dauke wutar lantarki tun da sanyin safiyar Lahadi, aka kuma rufe bankuna, asibitoci, filin jirgin sama da tashar jirgin kasa da sauransu a safiyar Litinin.

El-Rufai a wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Twitter ya ce, “Ana neman Ayuba Wabba da sauran shugabannin NLC na Kasa ruwa a jallo saboda manakisa ga tattalin arziki da kai wa kadarorin gwamnati hari da sauran laifuka.

“Duk wanda ya san inda suka boye ya sanar da Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna, akwai tukwici mai tsoka.”

Tun kafin fara yajin aikin gargadin dai bangarorin biyu ke ta maganganu da kakkausan lafazi, inda El-Rufai ya ce yajin aikin ko adawa ba za su sa a janye batun sallamar ma’aikatan ba.