✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya dakatar da Wazirin Zazzau

Gwamnatin Jihar Kaduna ta dakatar da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu.

Rahotanni na cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta dakatar da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu.

Dakatarwar da aka yi masa na kunshe cikin takardar da aka aike masa da sa hannun Babba Sakataren Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautun Jihar, Musa Adamu a madadin kwamishina Jafaru Sani.

Aminiya ta tuntubi Wazirin na Zazzau domin tabbatar da labarin amma nan take basaraken ya katse wayar bayan wakilinmu ya gabatar masa da kansa.

Amma wata kwakkwarar majiya mai kusanci da shi ta tabbatar wa wakilin namu cewa ya karbi takardar dakatarwarsa ranar Alhamis.

Aminiya ta ruwaito cewa masu zaben sarkin su biyar sun samu sabani da Gwamnatin Jihar Kaduna a lokacin aikinsu na zabar wanda zai gaji Sarkin Zazzau na 18, marigayi Alhaji Shehu Idris.

Masu zabar sarkin sun mika sunaye uku daga cikin masu neman kujerar; Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu; Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru; dan Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris domin gwamnan jihar ya sabi Sarkin Zazzau na 19 daga cikinsu.

Duk da cewa Gwamna Nasir El-Rufai ya ki amincewa da zabin da suka ka yi na farko, masu zabar sarkin sun sake mamaita zabin nasu a karo na biyu da ya umarce su su sake.

Amma duk da haka ya yi amfani da ikonsa ya nada Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli wanda makusancinsa ne a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Ana zargin takardar tuhuma da kuma dakatarwar da aka yi wa Wazirin Zazzau “na da nasaba da batun zaben sabon sarki bayan rasuwar Sarkinmu, marigayi Mai Martaba Alhaji Shehu Idris”, inji majiyar tamu.

Majiyar tamu ta fada ta ce rashin halartarsu zaman da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Masarautun jihar ya kira, “biyayya ce ga umarnin kotu.

“Kotun Mai Shari’a Kabir Dabo da ke Dogarawa, Zariya kan karar da Iyan Zazzau ya shigar na kalubalantar nada sarkin, ta ce kowa ya tsaya a matsayin da yake.”

Wazirin Zazzau shi ne shugaban Masu Zabar Sarki a Masarautar Zazzau tare da Limamin Gari, Alhaji Dalhatu Kasim; Limamin Kona, Muhammad Aliyu; Makama Karami, Alhaji Muhammad Abbas; da kuma Fagacin Zazzau, Alhaji Umar Muhammad.