✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

El-Rufai ya hana sayar da raguna a cikin unguwa

Idan masu sayar dabbobin ba su tashi ba, gwamnati za ta kwashe su

Gwamnatin Jihar Kaduna ta hana sayar da dabbobi a gefen hanya da sauran wuraren da ba a amince da su ba a cikin jihar.

Umarnin gwamnatin ya fito ne yayin da al’ummar Musulmi ke shirye-shiryen sallar layya.

Labarin hana sayar da dabbobin a gefen hanya ya janyo jita-jita a cikin jihar musamman a intanet inda wasu ke yada cewa wai gwamnatin ta hana shigowa ne da dabbobi daga wasu jihohi.

Kamar kowace sallar layya, masu sayar da dabbobi daga sassan kasarnan kan ziyarce garuruwa daban-daban, su killace wurare domin sayarwa ga wadanda Allah Ya ba su ikon yin layya.

Umarnin gwamnatin jihar

Sai dai kuma a bana, takardar gwamnatin jihar ta fitar dauke da sa hannun Hukumar Kula da Gidaje da Tsara Birane (KASUPDA) Ismail Umaru Dikko a ranar Talata, ta umurci masu sayar da dabbobi da ke zama gefen hanya a jihar da su kwashe dabbobin nasu ko kuma hukumar ta kwashe dabbobin.

A cikin takarda, Dikko ya ce, idan har ba a kwashe dabbobi zuwa kasuwannin dabbobibn ba cikin awa 24, to masu su za su yi asararsu in har gwamnati ta kai samame a haramtatun wuraren.

Wannan takardar kashedi da gwamnatin ta fitar ta haifar da jita-jitar cewa gwamnati ta hana shigowa da kuma sayar da dabbobi a Kaduna.

Masu dabbobi sun koka

Aminiya ta tattauna da masu sayar da dabbobi a sassan garin Kaduna, inda wakilinmu ya je titin Bashama Road, inda wani mai suna Mutari Uba, ya ce hukumcin gwamnatin ya yi tsauri.

Mutari wand ake zayar da dabbobi ya ce da yawa daga cikin masu sayar da ragunan daga wasu jihohi suka zo. Saboda haka ya roki gwamnatin da ta sassauta dokar.

“Ni mutumin Kano ne, na kwashe akalla shekara 15 ina kawo raguna wannan filin a duk shekara. Muna rokon gwamnati ta sasauta dokar nan”, inji shi.

Surajo Bashir, shi ma mai sayar da dabbobi ne, ya kwatanta matakin gwamnatin a matsayin rashin imani, saboda ba a tashi tayar da su daga wuraren sana’ar ba sai da suka baje hajarsu.

Surajo, ya ce a kofar gidansa yake sayar da ragunan, amma an ce ya mayar da su kasuwar Zango cikin awa 24, wadda a halin yanzu makil take da dabbobi.

Gwamnati ta yi daidai

A nasa bangare shugaban kungiyar masu sayar da raguna a Kasuwar Zango, Hassan Saleh, ya yaba da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, ya kuma yi kira ga masu sayar da dabbobin su koma can domin hana yaduwar COVID-19.