✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufa’i ya sallami masu rike da mukaman siyasa 99 daga aiki

Hakan dai na nufin an sallama kusan kaso 30 cikin 100 na masu rike da mukaman siyasa a jihar.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce ya sallami masu rike da mukaman siyasa 99 daga aiki a jihar.

Gwamnan, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ’yan jarida a Kaduna, ya ce wadanda ya sallama din sun kai kusan kaso 30 cikin 100 na masu rike da mukaman na siyasa a jihar.

Ya ce tuni jihar ta fara aiwatar da manufarta ta daidaita yawan ma’aikata, amma har yanzu ba ta kori ko da ma’aikacin Jihar daya ba.

El-Rufa’i ya ce ma’aikatun da ke da alaka da Kananan Hukumomi ne kawai aka sallama, wanda ya shafi Kananan Hukumomin Jihar 23, Hukumar Kula da Ilimin Bai Daya ta SUBEB da kuma Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko.

A cewar Gwamnan, rage ma’aikatan zai ci gaba kamar yadda aka tsara la’akari da yadda kason kudaden Jihar daga asusun tarayya ke raguwa a kullum.

“To sai dai ma’akatan da suke da alamar tambaya a bayanansu sai da muka basu damar su kare kansu kafin mu dauki kowanne irin mataki a kansu,” inji Gwamnan.

Kazalika, ya kuma ce gwamnatinsa ta dauki ma’akata sama da 11,000 a bangaren lafiya, Jami’ar Jihar ta KASU da kuma makarantun Firamare da Sakandire da ke Jihar.

A cewar Gwamnan, babu kamshin gaskiya a zargin da ake yi cewa galibin kudaden Jihar na tafiya ne wajen biyan masu rike da mukaman siyasa.

Ya kuma bayar da tabbacin cewar Jihar ba zata daina biyan mafi karancin albashi na N30,000 wanda ta jima da fara biya ba.