✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya sassauta dokar hana fita a kudancin Kaduna

An sassauta dokar daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safiyar kowace rana.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita ta awa 24 da ta sanyan a kananan hukumomin Kaura da Jema’a sakamakon tashin-tashina da aka yi a yankunan.

Hukuncin sassauta dokar daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe, ya biyo bayan rahoton fara daidaituwar al’amura a yankunan da jami’an tsaro suka gabatar wa gwamnatin jihar.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

A cewarsa an cimma matsayar yin zirga-zirga daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a yankunan, kana dokar ta ci gaba daga 6 na yamma zuwa 6 na safiya a kullum.

Kazalika, gwamnatin jihar ta yi barazanar sake dawo da dokar matukar mazauna yankunan suke bijirewa dokokin da aka shimfida musu.

Har wa yau, za a ci gaba da sanya ido kan yadda al’amura ke wakana a yankunan, don tabbatar da ba a sake samun tashin-tashina ba.