✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai zai gina ‘Film Village’ a Kaduna

Gwamnatin Kaduna da masu ruwa da tsaki sun rabbata hannu kan yarjejeniyar kafa alkaryar fina-finai (Film Village).

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da amincewarta da kafa alkaryar fina-finai da aka fi sani da Film Village.

Tuni gwamnatin ta sanya hannu a kan takardar yarjejeniyar gina cubiyar.

An sanya hannun ne a taron bunkasa kasuwanci da tattalin arziki na jihar wato Kaduna Economic and Investment Summit da ake ci gaba da yi a jihar.

Kwamishina kuma Magajin Garin Kaduna, Malam Muhammad Hafiz Bayero, ne ya sanya hannun tare da sauran masu ruwa da tsaki.

A sanarwar da Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar, ta ce alkaryar fina-finan za ta taimaka wajen bunkasa harkokin fina-finai.

A cewar sanarwar, alkaryar za ta samar da ayyuka ga jarumai da marubuta da masu kwalliya da sauran masu aikin bayan fage a fina-finai.

Idan ba a manta ba, a shekarun baya ne aka amince da gina alkaryar a Jihar Kano, amma wasu mutanen suka nuna rashin amincewarsu, wanda hakan ya sa dole gwamnatin jihar din ta bar batun.