✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Elon Musk Ya Saye Twitter ya kori jagororin kamfanin

Elon Musk yana kammala sayen Twitter ya sallami manyan shugabannin kamfanin

Jim kadan bayan saye kamfanin sada zumunta na Twitter, Elon Musk, ya sallami wasu daga cikin manyan jagororinsa daga aiki.

Musk dai ya kammala saye kamfanin da aka yi wa farshin Dala Biliyan 44, ya kuma fara da sallamar shugaban kamfanin Parag Agrawal.

Sauran jiga-jigan da aka sallama sun hada da Shugaban Sashin Shari’a Vijaya Gadde, da Shugaban Sashen Kudi, Ned Sega.

Sa’o’i kadan kafin wa’adin da kotu ta bayar na sayen kamfanin ya cika, ELon ya wallafa cewa ‘Tsuntsun ya samu ’yanci’ ta shafinsa na Twitter, wato dai yana magana kan tambarin kamfanin.

Haka kuma ya sauya bayanansa na shafin zuwa ‘Shugaban Twit’, da kuma mayar da wurin da yake zuwa Hedikwatar Twitter.

Shi ma dai shugaban kamfanin na baya Bret Taylor, ya wallafa a shafinsa na LinkedIn cewa ya ajiye aiki da kamfanin.

Musk, mai ikirarin shi “mai kare hakkin fadin albarkacin baki ne” ya sha sukar Twitter a baya, kan yadda ake gudanar da shi, da ma manufofinsa.

Kazalika sun samu sabani kan sharuddan mallakar kamfanin a baya, inda Musk ya zargi Twitter da bayar da bayanan da ba su dace ba game da lambobin masu amfani da kafar.