Daily Trust Aminiya - #EndSARS: ‘Ba za mu lamunci tayar da zaune tsaye da sunan za
Subscribe

Ministan Watsa labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed

#EndSARS: ‘Ba za mu lamunci tayar da zaune tsaye da sunan zanga-zanga ba’

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadin cewa ba za ta lamunci yunkurin fakewa da zanga-zangar #EndSARS a jefa Najeriya cikin halin kaka-ni-ka-yi ba.

Ministan Watsa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed shine ya aike da sakon gargadin lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na NTA a cikin wani shirinsu mai sun Weekend File a ranar Asabar.

A cikin shirin wanda ya mayar da hankali wajen tattauna batun zanga-zangar, ministan ya ce harin da aka kaiwa gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola lokacin da yake tsaka da jawabi ga masu zanga-zangar ya nuna karara cewa yanzu bata-gari sun karbe ragamarta.

A cewar ministan, ko da yake asalin wadanda suka kirkiro zanga-zangar sun yi ne da manufa mai kyau, yanzu ta bayyana ba su ke tafiyar da ita ba.

Ya ce, “Zanga-zangar lumana wata ginshiki ce a mulkin dimokradiyya, hakan ne ma ya sa Gwamnatin Tarayya a cikin kwanaki 11 da suka gabata ta kyale masu yi su ci gaba.

“Amma idan aka duba abinda ya faru da gwamnan jihar Osun, za a fahimci cewa gaba daya lamarin ya tashi daga zanga-zangar lumana ko kuma ta neman sassauci daga cin zarafin jami’an ‘yan sanda.

“Babu inda a duniya gwamnati za ta zauna ta nade hannuwanta tana kallon kasarta na neman fadawa cikin rikici.

“Yanzu fa ba wai da masu zanga-zangar #EndSARS muke fama ba, a’a, wasu zauna-gari-banza ne ke neman daukar doka a hannunsu.

“Saboda haka ya zama wajibi mu tashi tsaye wajen kare rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba,” inji ministan.

Alhaji Lai Mohammed ya kara da cewa yadda ake kara samun asarar rayuka da dukiyoyi na nuna cewa yanzu zanga-zangar ta tashi daga ta lumana.

Ya kuma zargi wasu da ya bayyana a matsayin marasa kishin kasa dake kokarin yin amfani da yanayin wajen aibata gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

More Stories