✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EndSARS: Babu wanda aka kashe a Lekki Tollgate, inji Gwamnatin Legas

Daga cikin shawarwari 32 na kwamitin, gwamnatin Legas ta amince da 11, za ta mika wa Gwamnatin Tarayya 14

Gwamnatin Legas ta yi fatali da ikirarin rahoton kwamitin binciken tarzomar EndSARS cewa sojoji sun aikata kisa a lokacin dambarwar a jihar.

Zargin sojoji da kashe masu zanga-zangar EndSARS a Lekki Tollgate na daga cikin manyan zarge-zargen da rahoton kwamitin binciken ya tabbatar, amma gwamnatin jihar ta yi watsi da shi.

Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar kan rahoton kwamitin ta bayyana zargin sojoji da kashe mutum tara a Lekki Tollgate da cewa hasashe ne, wanda babu hujjojin da ke tabbatar da shi, don haka ta yi watsi da shi.

A bara ne dai Gwamnatin Jihar Legas ta kafa kwamitin binciken, wanda ya gabatar da rahotonsa ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu, mako biyu da suka gabata.

Bayan nan ne kwafin rahoton mai dauke da kura-kurai ya rika yawo, wanda a ciki ya nuna sojoji da ’yan sanda sun aika laifuka.

Ya kuma nuna cewa an kashe mutum 11 a lokacin zanga-zangar a Lekki Tollgate, sannan ya shawarci gwamnatin jihar ta sauya sunan wurin zuwa EndSARS gami da karrama mutanen da tarzomar ta ritsa da su.

Sai dai gwamnatin jihar da ta ba kwamitin aikin ta yi watsi da wasu shawarwarin da kwamitin ya bayar a kan zargin kisan.

Daga cikin shawarwari 32 da kwamitin ya bayar, gwamnatin jihar ta karbi 11, ta yi wa shida gyaran fuska sannan ta yi watsi da guda daya.

A cewarta, sauran shawarwari 14 kuma ba ta da iko a kansu, saboda haka za ta gabatar da su ga Gwamnatin Tarayya ta dauki mataki a kansu.

A yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce yana jiran sakamakon binciken kwamitin, tuni Ministan Sadarwa, Lai Mohammed, ya yi watsi da rahoton, wanda ya kira tatsuniya.