✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: Bata-gari sun sace bindigar AK-47 100 a Legas

Kwamitin da Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya Muhammed Adamu ya kafa domin binciken barnar da aka yi wa rundunar a rikicin da ya biyo bayan…

Kwamitin da Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya Muhammed Adamu ya kafa domin binciken barnar da aka yi wa rundunar a rikicin da ya biyo bayan zanga zangar #EndSARS, ya ce batagari sun sace bindigar AK-47 akalla guda 100 a lokacin rikicin a Legas.

Shugaban Kwamitin CP Yaro Abutu ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar 7 ga watan Nuwamba, inda ya ce kwamitin na ci gaba da tattaro bayanan barnar da rikicin ya janyo.

Kwamitin ya ce batagarin sun kuma sace alburusai na bindiga guda 2600, a lokacin da suka kai wa ofishin runduna ta 37 hari da kuma barnata motocin ’yan sanda 367 ciki har da motoci masu sulke 10 da kuma motocin sintiri na Hilux da tarin kananan motoci da suka kona a Legas a sa’ilin tarzomar da ta biyo bayan zanga zangar ta #EndSARS.

CP Yaro ya ce abin takaicin ne ganin yadda barnar tazo a karshen shekara lokacin da ake samun karuwar kalubalen tsaro.

“Muna ci gaba da rangadi a jihohin 17 da aka kai wa jami’ai hari da kuma ofisoshisu, kasancewar Jihar Legas ce tamkar cibiya da aka lalata akalla kaso 30 na kadarorin rundunar ’yan sanda, don haka muka fara da ita”, inji shi.

Ya kara da cewa “akwai bukatar duk wanda ya san akwai makaman a hannunsa ya yi hanzarin maido su ga ofishin jami’an hukumar mafi kusa ko ya kai wa shugabannin al’ummar yankin da yake.”

Ya bukaci jama’a da su rika ankarar da jami’an rundunar da zarar sun ci karo da ire-ire wadannan makamai.

“Akwai makamai uku da aka dawo da su a ranar Juma’a 7 ga watan Nuwamba, daya daga ciki jama’a ne suka gano kuma an karar da jami’anmu, don haka muke kara kira da a bamu hadin kai.”

Ana sa ran kwamitin na mutum 10 zai mika sakamakon binciken shi ga babban Sufenton ’yan sanda cikin makonni uku masu zuwa.