✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: Kungiyoyin matasan Arewa sun nemi a yi taron gaggawa

Shugabannin Kungiyoyin Matasan Arewa (APAY), sun nemi a dakatar da zanga-zangar #EndSARS saboda matsalolin da ke tattare da ita, domin a yi zaman tattaunawa don…

Shugabannin Kungiyoyin Matasan Arewa (APAY), sun nemi a dakatar da zanga-zangar #EndSARS saboda matsalolin da ke tattare da ita, domin a yi zaman tattaunawa don magance muhimman matsoloin da yankin ke fuskanta. 

Shugaban APAY, Abubakar Isa Bakori ya shaida wa taron ’yan jarida a Kano cewa ya zama tilas kungiyoyin su hada kai duba da yadda yankin ke ci baya ta kowace fuskar kuma zanga-zanga ba za ta magance matsalolin a yanzu ba.

Ya kara da cewa hadakar kungiyoyin ta yanke shawarar gudanar da taron gaggawa da zai samu halarcin gwamnoni da zababbun ’yan Majalisar Tarayya da jihohi, shugabannin al’umma, malaman addinai da dai sauransu.

Sanarwar ta zargi akasarin zababbun gwamnoni tun daga 1999 da hannu a cikin halin tabarbarewar da jihohin Arewa suke cikin a yau.

“Mafi yawancinsu sun mayar da hankali ne wajen gina siyarsarsu ne ba gina jihohinsu ba.

“Da haka suka kawo rarrabuwar kai da rashin yarda da juna da suka hairfar da rikice-rikicen addini da na kabilanci a jihohin.

“Da wannan mu ke son a yi taro don samun mafita, amma zanga-zanga ba mafita ba ce”, inji shi.

Ya ce taron taron gaggawan da za a gudanar shi ne: “Su wa za su yi magana da yawun Arewa?

“Mun kuma yanke hukunci cewa duk gwamnan da ya ki harlartar taron ba tare da kwakkwaran dalili ba a matsayin makiyin Arewa da cigabanta kuma za mu yi maganinsa lokacin zabe”, inji shi.