✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

#EndSARS: ‘Masu zanga-zanga’ sun kona ofishin karamar hukuma

'Masu zanga-zangar #EndSARS' sun banka wa Sakatariyar Ajeromi Ifelodun wuta

Wasu da ake zargin bata-gari ne da suka saje a zanga-zangar #EndSARS sun banka wa Sakatariyar Karamar Kukumar Ajeromi Ifelodun ta Jihar Legas wuta.

Sakataren Watsa Labarai na Karamar Hukumar, Sheriff Fakunle ya ce da misalin karfe 1:13 na ranar Talata bata-garin suka kai harin, suka sace tare da barnata dukiyoyi na miliyoyin Naira.

“Yanzu haka daruruwan matasa ne dauke makamai suka yi wa ofishin karamar hukumar kawanya suna satar kayayyaki kana suka banka wuta, sun kona motoci da dama a harabar ofishin”, inji shi.

Matasan sun kuma sun kona ofishin ‘yan sanda da ke Leyeni a karamar hukumar ta Ajeromi Ifelodun.

Mashawarcin Shugaban Karamar Hukumar kuma mazaunin yankin, Malam Musa Nice, ya shaida wa Aminiya cewa matasan sun kwashe duk kayayyakin da ke ofishin Shugaban Karamar Hukumar.

Wannan lamarin na zuwa ne bayan Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya ayyana dokar hana fita a jihar saboda rikidewar da zanga-zangar #EndSARS ta yi zuwa fadace-fadace da kone-kone.