✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: MDD ta ja kunnen Najeriya kan kashe masu zanga-zanga

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterras ya yi kira ga gwamnatin Najeriya kan ta kawo karshen cin zalin jama’a

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterras ya yi kira ga gwamnatin Najeriya kan ta kawo karshen cin zalin jama’a da ‘yan sanda suke yi kan masu zanga-zangar #EndSARS.

Ya yi Allah-wadai da yadda ake ci gaba da kai hari kan wadanda ba su ji ba ba su gani ba, musamman na ranar Talata a Legas wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkatar wasu daga cikinsu.

Mista Guterras ya bayyana hakan ne a wani sako da babban jami’in sashen bayar da agaji na hukumar a Najeriya, Edward Kallon ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata.

Ya kuma jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su, yana mai kira ga hukumomin Najeriya kan su gudanar da cikakken bincike tare da gurfanar da masu hannu a lamarin gaban kuliya.

Babban sakataren ya kuma yi kira ga jami’an tsaron da su ci gaba da kare rayukan jama’a yayin da su kuma masu zanga-zangar ya bukace su da su ci gaba da yin ta cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin kan ta bullo da hanyoyin yayyafawa kurar rikicin wuta.

Ya ce majalisar tasu a shirye take ta tallafawa Najeriya wajen gano bakin zaren.

Kusan makonni biyu kenan da kasar ke fuskantar tashin-tashina sakamakon zanga-zangar neman rushe sashen ‘yan sanda na SARS wacce bisa ga dukkan alamu yanzu ta rikide zuwa rikici.