✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ENDSARS: Najeriya ta gana da jakadun Amurka da Birtaniya

Ana sa ran taron zai tattauna kan zanga-zangar ENDSARS da ke yaduwa tare da sauya salo

Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, ya fara zama da jakadun kasashen waje a Abuja.

Ana sa ran taron zai tattauna ne kan zanga-zangar ENDSARS da ke yaduwa tana kuma sauya salo a Najeriya.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai jakadun Amurka da Ingila da Janus da dai sauransu.

Da farko an gayyaci ’yan jarida amma daga bisani aka soke gayyatar.

Najeriya na cikin yanayin zanga-zangar nuna fushi kan kisan gilla da cin zarafi da ’yan sanda suka rika yi wa mutane a baya.

Makonni biyu da suka gabata, kasashen ketare sun nuna rashin amincewarsu ga cin zarafi da tauye hakkin bil’Adama da ake yi a Najeriya da kuma halin ko in kula da gwamnati take nunawa.