Daily Trust Aminiya - #EndSARS: Osinbajo ya bukaci masu zanga-zanga su mayar da wu
Subscribe

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo

#EndSARS: Osinbajo ya bukaci masu zanga-zanga su mayar da wuka cikin kube

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya nemi afuwar ‘yan Najeriya tare da amincewa gwamnatinsu ba ta yi gaggawa ba wajen biyan bukatun masu zanga-zangar kawo karshen rundunar tsaro ta SARS.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Osinbajo ya ce, “Ya ku ‘yan Najeriya, na san da yawa daga cikinku sun fusata, kuma suna da dalilin yin fushin. Ya kamata ace mun amsa kiranku cikin gaggawa, a saboda haka muna neman afuwarku.

“In da cikakkiyar masaniya kan yadda matasa suke ji, da yawa daga cikinsu na jin kawai mun yi shiru ba mu ce uffan ko mun yi abinda ya kamata ba, suna da dalilin yin hakan.

“Akwai mutane da dama da aka ci zarafinsu ta hanyar ayyukan ‘yan sanda, kuma wannan abu ne da ba za mu lamunta ba.

“Dole ne mu dauki nauyin kare rayukan al’ummarmu, wani lokacinma har daga hannun wadanda aka dauke su domin su kare rayuwar tasu,” inji Osinbajo.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma yi amannar cewa zanga-zangar ta wuce ta neman a rushe rundunar SARS, inda ya bayar da tabbacin cewa gwamantinsu na yin duk mai yuwuwa wajen ganin ta inganta ayyukan ‘yan sandan ta hanyar bunkasa walwalarsu da samar musu da kayan aiki da kuma horo a kai a kai.

Farfesa Osinbajo ya ce ya gudanar da taro da masu ruwa da tsaki iri-iri domin ganin an magance matsalolin da suka tunzura matasan har suka fito zanga-zangar, ciki har da shirya taro da gwamnonin Najeriya 36 da kuma ministan Babban Birnin Tarayya Abuja kan lamarin.

Daga nan sai ya bayar da tabbacin cewa dakarun rundunar ta SARS da aka rushe ba za su shiga sabuwar da aka maye gurbi da ita ta SWAT ba.

More Stories