✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: Rarara ya saka kyautar Motoci da kudade a gasar Mawaka kan zaman lafiya

Biyo bayan bukatar da gwamnan Kano ya yi ga fitaccen Mawakin siyasar nan na Arewacin Nijeriya Dauda Kahutu Rarara, kan ya yi amfni da fasahar…

Biyo bayan bukatar da gwamnan Kano ya yi ga fitaccen Mawakin siyasar nan na Arewacin Nijeriya Dauda Kahutu Rarara, kan ya yi amfni da fasahar da Allah ya bashi wurin wayar da kan jama’a akan muhimmancin da zaman lafiya ke da shi a tsakanin Al’uma.
Gwamnan ya bayyana haka a wata gana wa da ya yi a daren litinin da kungiyar Mawaka da masu shirya fina-finan Hausa ta MOPAN a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin Kano.
A nasa bangaren mawaki Rarara, ya mika godiyarsa ga gwamnan bisa damar da ya ba shi ta fadakar da jama’a, nan take kuma ya shirya wata gagarumar gasar mawaka da za su yi gasar waka kan zaman lafiya.
Rarara, ya karkasa Mawakan zuwa rukuni uku da wani rukuni daban na masu wasan barkwanci, kuma kowane rukuni na masu gasar yana dauke da mutane 20 kamar haka:
  1. Mawakan Hausa na gargajiya
  2. Mawakan Siyasa da fina-finai
  3. Mawakan Ingausa na Hi hop
  4. Masu wasannin barkwanci
Mawakin ya yi alkawarin bayar da kyaututtuka ga dukkan wandanda suka shiga gasar kamar haka:
  •  Wadanda suka zo na daya daga kowane rukuni suna da kyautar Mota
  •  Wadanda suka zo na biyu daga kowane rukuni kyautar Babur mai kafa uku (Adaidaita sahu)
  •  Wadanda suka zo na uku daga kowane rukuni kyautar Babur mai kafa biyu
  •  Wadanda suka zo na 4 zuwa na 10 daga kowane rukuni za su samu kyautar kudi naira duba 150,000
  • Wadanda suka zo na 11 zuwa na 20 daga kowane rukuni za su samu kyautar kudi naira duba 100,000
Dauda Rarara, ya shirya gasar ne saboda ya karfafin shirin gwamnatin Kano na wayar da kai da fadakar da jama’a kan alfanun da zaman lafiya ke da shi a cikin al’uma.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake samun karancin zaman lafiya a wasu jihohi a Nijeriya, sakamakon zanga-zangar Endsars da aka fara gudanar da it makonni biyu da suka gabata.